Isa ga babban shafi
Wasanni

Seria A: An ci tarar kungiyar Verona euro dubu 20,000

Hukumar lura da gasar Seria A, ta ci tarar kungiyar Verona euro dubu 20,000, sakamakon yadda wasu magoya bayanta suka rika ihun furta kalaman nuna wariyar launi, ga dan wasan tsakiya na Juventus Matuidi.

Dan wasan kungiyar Juventus Blaise Matuidi a lokacin da ya jefa kwallo a ragar Verona, mintuna 6 da fara wasa.
Dan wasan kungiyar Juventus Blaise Matuidi a lokacin da ya jefa kwallo a ragar Verona, mintuna 6 da fara wasa. AFP/Getty Images
Talla

Magoya bayan na Verona sun fara muzanta Matuidi ne bayanda ya zura kwallo a ragarsu mintuna 6 da fara wasan, wanda a karshe Juventus din ta lallasasu da 3-1.

Haka ya sa a lokacin da yake yanke hukuci ka, Alkalin kotun sauraron kararrakin wasannin da ke Italiya Gererdo Mastrandrea, ya kara da cewa tilas kungiyar kwallon kafar ta Verona, ta buga wasa guda, ba tare da magoya bayanta sun shiga kallo ba, baya ga biyan tarar ta euro 20,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.