Isa ga babban shafi
Wasanni

“Yan wasan Najeriya sun nuna kwazo wajen zura kwallaye a Ingila”

Wani rahoton hukumar gasar Premier ta Ingila, ya nuna cewa Najeriya ce ta goma, a jerin kasashen duniya da ‘yan wasansu suka fi zura kwallaye a gasar kwallon kafar ta Ingila a shekarar 2017.

Dan wasan Super Eagles ta Najeriya kuma dan wasan kungiyar Manchester City, Kelechi Iheanacho
Dan wasan Super Eagles ta Najeriya kuma dan wasan kungiyar Manchester City, Kelechi Iheanacho The Sun
Talla

An dai tattara rahoton ne ta hanyar yin la’akari da yawan cin kwallaye da kuma kwarewar ‘yan wasan na kasashe daban a gasar ta Premier.

‘Yan wasan Najeriya sun samu mataki na 10 ne, bayan zura kwallaye 471 a shekarar 2017, hakan ya basu damar zarta kwazon takwarorinsu na kasashen Brazil, Argentina, Italiya da kuma Jamus.

‘Yan wasan kasar Ingila ke kan gaba wajen zura kwallayen da yawansu ya kai 10,826. Sai na Faransa a matsayi na biyu, bayan cin kwallaye dubu 1,477, yayinda ‘yan wasan Jamhuriyar Ireland suke a matsayi na uku, bayan zura kwallaye 945 a gasar ta Premier.

A nahiyar Afrika kuwa, bayan ‘yan wasan Najeriya da suke a matsayi na daya kuma na 10 a duniya, Ivory Coast ce kasa ta 14, bayanda ‘yan wasanta suka zura kwallaye 321 a gasar Ingilan.

Sai kuma ‘yan wasan Senegal a matsayi na 15 da kwallaye 314.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.