Isa ga babban shafi
Wasanni

Jami'an da ke shirya wasannin Premier suna rashin adalci - Wenger

Mai horar da kungiyar Arsenal Arsene Wenger, ya zargi jami’an da ke shirya wasannin gasar Premier ta Ingila, da nuna son kai ciki kakkausan harshe.

Mai horar da kungiyar Arsenal Arsene Wenger.
Mai horar da kungiyar Arsenal Arsene Wenger. Reuters/Michael Dalder
Talla

Wenger ya bayyana haka ne, bayan wasan da aka tashi tsakanin kungiyarsa da West Brom, wanda aka tashi kunnen doki 1-1.

A cewar Wenger, da akwai shakku hatta kan adalcin masu alkalancin wasanni, wadanda yace ayyukansu na tattare da matsaloli, sai kuma tsari ko shirya jadawalin wasannin Premier, da yace jami’an da nauyin hakan ya rataya a wuyansu sun fifita wasu kungiyoyin.

Mai horar da Arsenal din ya yi zargin cewa tuni jami’an shirya wasannin, suka shirya bai wa kungiyar Chelsea damar samun nasara kan ta Arsenal, a wasan da zasu fafata ranar Laraba mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.