Jamus ta ci gaba da rike kanbinta a jadawalin FIFA
Jamus da Brazil sun ci gaba da rike matsayinsu na ɗaya da na biyu a jerin ƙasashen da suka fi iya shafa ƙwallon ƙafa a duniya.
Wallafawa ranar:
Hakan na ƙunshe ne a cikin sabon jadawalin ƙasashe masu buga ƙwallon ƙafa da hukumar FIFA ta fitar, a watan Nuwamba, 2018.
Portugal ce ta 3 a cikin jerin, yayin da Argentina ke a matsayi na 4, sai kuma Belgium a matsayi na 5.
Senegal wadda ke a matsayi na 23 a duniya ita ce ta ɗaya a nahiyar Afirka. Tunisia na biye mata a matsayi na 27 a duniya kuma ta biyu a Afirka, yayin da Masar ke a matsayi na 3 a Afirka.
Kamaru ce ta 7 a Afirka, sai Ghana a matsayi na 8, Najeriya kuma na a matsayi na 9, inda a duniya kuma take a matsayi na 51.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu