Isa ga babban shafi
Wasanni

'Yan sandan Masar sun sallami magoya bayan Zamalek 236

Jami’an tsaron kasar Masar sun saki sama da magoya bayan kwallon kafa dari biyu da suka tsare su sama da watanni biyar.

Magoya bayan kungiyar Zamalek yayin da suke jifan jami'an tsaro da duwatsu a fiilin wasa na Borg El Arab, da ke Alexandria, yayin wasa tsakanin Zamalek da Al-Alhi ta kasar Libya, wanda aka tashi 2-2.
Magoya bayan kungiyar Zamalek yayin da suke jifan jami'an tsaro da duwatsu a fiilin wasa na Borg El Arab, da ke Alexandria, yayin wasa tsakanin Zamalek da Al-Alhi ta kasar Libya, wanda aka tashi 2-2. REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Talla

‘Yan sandan kasar sun kame magoya bayan kungiyar Zamalek 236 ne, yayinda kungiyar ta fafata wasa da takwararta ta Al-Alhi SC ta Libya ranar 9 ga watan Yuli da ya gabata wasan da aka tashi 2-2, inda ake zarginsu da tada yamutsi, lalata filin wasa, da kuma kai wa jami’an ‘yan sanda hari.

Bayan shafe watanni ana gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake musu ne, rundunar ‘yan sandan Masar din ta yanke shawarar sakinsu, ganin cewa an samun cikakkun shaidun da zasu tabbatar da zargin da ake musu, da zai kai ga gurfanarsu a gaban kotu.

A shekarar 2015 gwamnatin Masar ta haramta kungiyoyin magoya bayan kwallon kafa na kasar masu tsattsauran ra’ayi, saboda gudunmawar da suka bayar, na zama a gaba-gaba cikin dubban masu zanga-zangar da suka yi sanadin hambarar da gwamnatin shugaban kasar Hosni Mubarak a shekarar 2011.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.