Isa ga babban shafi
Wasanni

Zidane ya gargadi masu caccakar Cristiano Ronaldo

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya yi gargadi, kan caccakar Cristiano Ronaldo da ke saran lashe kyautar Ballon d’or a cikin wannan makon karo na 5.

Zinédine Zidane
Zinédine Zidane AFP PHOTO/ GERARD JULIEN
Talla

Kwallaye 2 a cikin wasanni 10 na la liga Ronaldo ya zura a wannan kakar da suke fadi tashi, ganin cewa akwai ban-bancin maki 8 tsakaninsu da Barcelona da ke jan ragamar teburin.

Sai dai Ronaldo yana kan gaba wajen yawan kwallaye a zakarun Turai, inda ya zura kwallo 8 a wasanni 5 wanda Zidane ke saran a la liga ma zasu farfado.

Zidane ya ce 'daman a koda yaushe idan mutane basu samu yadda suke so ba sai suka da caccaka ya biyo baya.' Kallaman kocin na zuwa ne gabanni fafatawarsu na yau talata a Borussia Dortmund.

Shi ma karim Benzema a wannan kaka, kwallo na masa wuyar shiga raga. Abinda ya sa wasu irin kocin Valencia, Marceliono Garcia, ke cewa tawagar Madrid ta yi rauni a wannan kaka saboda rashin Alvaro Morata da James Rodriguez da Pepe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.