Isa ga babban shafi
wasanni

"Ya kamata 'yan Manchester United su zuki sigari"

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce, kamata ya yi su zuki tabar sigari saboda nasarar da suka samu akan Watford a fafatawarsu ta jiya a gasar Firimiya ta Ingila, in da suka ta shi ci 4-2.

Kocin Manchester United, Jose Mourinho
Kocin Manchester United, Jose Mourinho Reuters/Darren Staples
Talla

Manchester United ce ta fara zura kwlallaye uku, yayin da Watford ta farke kwallaye biyu a minti na 77 da kuma 84, amma daga bisani Jesse Lingard ya ci wa Manchester Kwallo ta hudu.

Ashley Young ne dai ya ci wa Manchester United kwallaye biyu a mintina na 19 da kuma 25, kuma Mourinho ya ce, a yanzu Young na taka leda cin kwarewa fiye da yadda ya ke yi a can baya.

Manchester United da ta sha kashi a wasanninta guda biyu da ta yi da Huddersfield da Chelsea, ita ce ta biyu a teburin gasar ta Firimiya a Ingila, in da ta ke bin bayan Manchester City.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.