Isa ga babban shafi
Wasanni

AC Milan ta kori kocinta daga bakin aiki

Kungiyar kwallon kafa ta AC Milan ta maye gurbin kocinta Vincenzo Montella da Gennaro Gattuso, bayan zarginsa da rashin tabuka abin kirki a wasannin da kungiyar da buga cikin wannan kaka.

Korarren Kocin kungiyar kwallon kafa ta AC Milan Vincenzo Montella.
Korarren Kocin kungiyar kwallon kafa ta AC Milan Vincenzo Montella. Reuters Media Express
Talla

AC Milan wadda yanzu haka ke matsayi na 7 da maki 20 a teburin Serie A ta yi rashin nasara a shidda daga cikin manyan wasanninta 14 a kakar bana, yayin da ta yi nasara a sau biyu kacal a wasanni taran da ta buga.

Ko a jiya Lahadi ma kungiyar ta tashi canjaras a wasan da ta buga tsakaninta da Torino a gida.

Gattuso mai shekaru 39 dan kasar Italiya wanda tsohon dan wasan kungiyar ta AC Milan ne da ya taka leda tsakanin shekarun 1999 zuwa 2013, ya kuma dauki Kofin gasar Serie A da na zakarun Turai sau biyu.

A gobe Talata ne kuma zai bayyana a wani taron manema labarai a filin atisayen kungiyar ta AC Milan.

Tuni dai Montella ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa sam bai yi bakin ciki da matakin na AC Milan ba hasalima martaba ce agareshi tsawon lokacin da ya dauka yana horar da ‘yan waasanta.

A baya dai AC Milan ta dauki kofin Serie A sau 18 yayinda ta dauki na zakarun Turai sau bakwai, amma tun daga 2013 ta gaza shiga cikin manyan kungiyoyi 3 na gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.