Isa ga babban shafi
Wasanni

Najeriya ta kafa tarihi a gasar kwallon tebur ta duniya

Hukumar kula da kwallon tebur ta Duniya, ITTF, ta yabawa Najeriya, sakamakon armashin da gasar kwallon tebur din da ta karbi bakunci ta yi, wato Nigeria Open, inda ta kafa tarihin zama ta farko da aka fi kallo daga sassan duniya.

Omar Assar na kasar Masar yayin fafata wasan kwallon tebur.
Omar Assar na kasar Masar yayin fafata wasan kwallon tebur. ittf.com/Hussein Sayed
Talla

A watan Agustan da ya gabata ne gasar kwallon Tebur din ta Nigeria Open ta gudana a birnin Legas, inda kasashen suniya 22 suka fafata tsawon kwanaki 5.

Sama da mutane daga sassan duniya miliyan 29. Dubu 35 ne suka kalli wasan kamar yadda binciken kafafen yada labarai ya nuna, hakan yasa gasar ta zama mafi kayatarwa da tafi yawan masu kallo a duniya.

Hakan yasa hukumar kwallon tebur din ta duniya ITTF ta goyi bayan najeriya ta sake daukar nauyin gasar da za’a yi a watan Agustan shekara ta 2018.

A gasar da aka kammala ta 2017, Omar Assar na kasar Masar ne ya lashe kofin bayan lallasa takwaransa na India Sarthak Gandhi da kwallaye 11-6, 13-11, 11-6, da kuma 11-18.

Yayinda a jin mata Dina Mesraf yar kasar Morocco ta lashe kofin, bayan lallasa ‘yar kasar Rasha Olga Kulikova da kwallaye 11-4, 16-4, 12-10, da kuma 11-6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.