Isa ga babban shafi
Wasanni

'Yan mata 70 zasu fafata a gasar tseren gudu da takalmi mai tsini

‘Yan mata 70 ne zasu fafata a wata gasar tseren gudu ta musamman, da zata gudana a birnin Legas da ke kudancin Najeriya a ranar 18 ga watan Nuwamba da muke ciki.

Wasu mata da ke tsala gudu yayinda suke sanye da takalma masu tsini.
Wasu mata da ke tsala gudu yayinda suke sanye da takalma masu tsini. Bogdan Cristel/Reuters
Talla

Gasar tseren da ta banbanta da wadanda aka saba gani, ‘yan matan zasu yi ta ne yayinda suke sanye da takalmi mai tsini, wanda tsawonsa zai kai akalla inci 4.

Shugaban shirya gasar Dede Kalu, ya ce makasudin shirya gasar shi ne taimakawa mata su kware wajen iya gudu da takalma masu tsini yayin tsallaka manyan tituna don kaucewa bugewar mota, kamar yadda hakan ta taba faruwa da wata da ya gazaya da ita asibiti.

Shekarun ‘yan matan da zasu fafata a gasar tseren gudun na tsakanin shekaru 17 zuwa 28. Kuma wadda tazo ta daya zata lashe kyautar Naira dubu 100, dubu 70 ga ta 2 sai kuma ta 3 da zata samu kyautar Naira dubu 50.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.