Isa ga babban shafi
Wasanni

An haramtawa shahararriyar 'yar wasa shiga tsere tsawon shekaru 4

Hukumar yaki da shan kwayouyin karin kuzari tsakanin masu wannin motsa jiki ta kasar Kenya, ta haramtawa ‘yar kasar, Jemima Sumgong shiga gasar gudu tsawon shekaru 4.

Jemima Sumgong 'yar kasar Kenya a lokacin da ta lashe lambar Zinare a gasar Olympics ta 2016 a birnin Rio na Brazil.
Jemima Sumgong 'yar kasar Kenya a lokacin da ta lashe lambar Zinare a gasar Olympics ta 2016 a birnin Rio na Brazil. REUTERS/Dylan Martinez
Talla

Jemima ta fuskanci hukunci ne bayanda hukumar ta same ta da laifin shan wata kwayar Karin kuzari da aka haramta amfani da ita a tun a shekarar 2012.

Idan za’a iya tunawa Jemima Sumgong ce ta lashe lambar zinare a gasar tseren gudu na yada kanin wani ajin mata, a gasar Olympics ta wannan shekara da ta gudana a birnin London.

Yayinda ta ke kare kanta, Jemima ta shaidawa kotun sauraron kararrakin wasanni cewa, an bata kwayar ta EPO ce a asibiti a dalilin juna biyun da take dauke da shi,  sai dai bayan da aka gudanar da bincike sai aka gano cewar takardun asibitin da ta gabatar na jabu ne.

Jemima Sumgong ita ce ‘yar kasar Kenya ta farko a mata da ta fara lashe lambar Zinare a gasar tseren gudun yada kanin wani da ke gudana a wasannin Olympics.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.