Isa ga babban shafi
Wasanni

Kwallon kafa: Ana daf da shafe tarihin da aka kafa a China

Ana sa ran wasan karshe tsakanin Ingila da Spain, da za’a buga ranar Asabar a kasar India, na cin kofin gasar cikin kwallon kafa ta duniya ajin ‘yan kasa da shekaru 17, ya kafa tarihin zama gasar da ta fi samun yawan masu kallo a tsawon tarihin farata a duniya.

'Yan wasan Spain yayin da suke murnar samun nasara na Mali a wasan kusa da na karshe da suka buga agasar cin kofin duniya na 'yan kasa da shekaru 17 a filin wasa na DY Patil da ke Mumbai, ranar 25 ga Oktoba, 2017.
'Yan wasan Spain yayin da suke murnar samun nasara na Mali a wasan kusa da na karshe da suka buga agasar cin kofin duniya na 'yan kasa da shekaru 17 a filin wasa na DY Patil da ke Mumbai, ranar 25 ga Oktoba, 2017. REUTERS/Danish Siddiqui
Talla

Kafin wasan karshen, za’a fara ne da fafatawar neman na uku tsakanin Mali da Brazil a ranar ta Asabar.

Jami’an da ke lura da gudanar gasar sun ce, suna sa ran mutane 67,000 ne zasu halarci kallon wasannin da zasu gudana a birnin Kolkata.

Kididdiga ta nuna cewa mutane miliyan 1.22 ne suka halarci kallon wasanni 50 da aka buga a gasar ta cin kofin duniyar ya ‘yan kasa da shekaru 17.

Hakan ke nuna Karin mutane kalilan ake bukata gasar ta shafe tahirin da aka kafa a shekara ta 1985 inda jimillar mutane miliyan 1.23 suka kalli wasannin da aka buga a gasar cin kofin duniya ajin ‘yan kasa da shekaru 16, da ta gudana a kasar China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.