Komitin Kwallon Kafa Na Africa Ya Hana Kenya karban Gasan cin Kofi Na 2018.
Bayan wani taron komitin zartaswa dake shirya gasan wasan kwallon kafa na cin kofin Zakaru na nahiyar da aka yi a Accra na kasar Ghana, an dakatar da kasar Kenya daga karban bakuncin gasan kwallon kafa na cin kofin nahiyar a shekara ta 2018.
Wallafawa ranar:
Ahmad Ahmad daga kasar Madagascar, wanda shine shugaban komitin ya bayyana cewa tafiyar hawainiya wajen shirin gasan wasannin ya sa aka kwace daga kasar Kenya.
Komitin ya gano cewa duk da cewa tsakanin watan Janairu zuwa Fabrairu za’a yi gasan, hukumomi a kasar Kenya sun sami kammala filin wasa daya ne kawai daga cikin filayen wasanni hudu da aka tsara za'a yi wasan a ciki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu