Za a kara tsakanin Ghana da Najeriya don daukar kofin WAFU
A jiya alhamis aka buga wasannin zagayen gaf da na karshe domin daukar kofin kwallon kafa na yammacin Afrika wato WAFU, a gasar da ake ci gaba da yi a birnin Cape Coast na kasar Ghana.
Wallafawa ranar:
A wasan na jiya, Nigeria ta doke Jamhuriyar Benin ci daya mai ban haushi, yayin da Ghana ta doke Niger ci biyu da nema.
Za a yi fafatawar karshe ne a ranar lahadi domin daukar wannan kofi tsakanin Ghana da Nigeria, yayin da Niger za ta fatafa da jamhuriyar Benin domin neman matsayi na uku a tsakaninsu.
Ana bayar da tukuicin dalar Amurka dubu dari daya ga kasar da ta dauki wannan kofi, sai kuma dala dubu 50 ga wadda ta zo a matsayin ta biyu, yayin da kasar da ta zo ta uku ke samun kyautar dala dubu 25.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu