Isa ga babban shafi
wasanni

Ya kamata a soke gasar Legue Cup a Ingila- Mourinho

Mai horar da tawagar kwallon kafa ta Manchester United, Jose Mourinho ya bukaci soke gasar League Cup a Ingila, in da ya ce, kwallon kafa za ta fi inganta a kasar muddin aka soke gasar.

Jose Mourinho na Manchester United
Jose Mourinho na Manchester United Reuters/Jason Cairnduff
Talla

Kalaman Mourinho na zuwa bayan watanni bakwai da ya jagoranci kungiyarsa har ta lashe kofin wannan gasa.

Sannan kuma a jiya ne Manchester United mai rike da kambi ta doke Burton da ci 4-1 a karawar da suka yi a gasar ta League Cup.

Amma duk da haka, Mourinho ya ce, illolin da gasar ke haifarwa sun zarta alfanunta.

Sau hudu Mourinho ke lashe gasar League Cup, in da ya lashe sau uku a lokacin da ya ke horar da Chelsea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.