Isa ga babban shafi
wasanni

Madrid ta sha kashi a hannun Real Betis

Kungiyar kwallon kafa ta Real Betis ta doke Real Madrid da ci daya mai ban haushi a fafatawar da suka yi a jiya a Laraba a gasar La Liga.

Cristiano Ronaldo na Real Madrid na cikin tawagar da ta sha kashi a hannun Real Betis
Cristiano Ronaldo na Real Madrid na cikin tawagar da ta sha kashi a hannun Real Betis REUTERS/Sergio Perez
Talla

Real Madrid ta sha kashin ne duk da cewa, gwarzon dan wasanta Christiano Ronaldo ya buga wasan bayan dawowarsa daga hutun dole.

Dan wasan Real Betis Antonio Sanabria ne ya yi nasarar cilla kwallon daya tilo a minti na 93 ana dab da tashi wasan.

A karon farko kenan cikin wasanni 74 da Real Madrid da ta kasance zakara a Turai ta gaza jefa kwallo ko da guda a wata fafatawa.

Sannan a karon farko kenan tun shekarar 1998 da Real Betis ke doke Real Madrid a gidanta, wato a Santiago Bernebeu.

Bayan wannan rashin nasara, yanzu haka Real Madrid na can kasan Barcelona mai jan ragama a teburin gasar ta La Liga, kuma tana da maki 8.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.