Isa ga babban shafi
Wasanni

FIFA ta haramtawa shugaban yankin Caribbean shiga wasanni

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta haramtawa shugaban hukumar kwallon kafa na Yankin Caribbean Gordon Derrick, shiga cikin al’amuran wasanni har tsawon shekaru 6, saboda samunsa da laifukan da suka shafi saba ka’idojin da’ar aiki da FIFAr ta gindaya.

Shugaban hukumar FIFA, Gianni Infantino.
Shugaban hukumar FIFA, Gianni Infantino. Reuters / Matthew Childs
Talla

Zalika shugaban zai kuma biya tarar dala 31,154.

FIFA ta ce laifukan Derrick ke aikatawa sun hada da nuna son zuciya yayin gudanar da aikinsa, bayarwa da kuma karbar kyautuka hadi da neman alfarma ba bisa ka’ida ba, aikata almundahana a fannin da ya shafi tasarrufi da kudade, sai kuma sabawa umarnin hukumar ta FIFA a lokuta daban-daban.

A shekarar da ta gabata Derrick ya yi yunkurin karbe iko da shugabancin hukumomin kwallon kafar arewacin Amurka, tsakiyar Amurkan ya kuma cigaba da rike nasa mukamin na shugabancin hukumar yankin Caribbean, bayan da aka samu shugabannin hukumomin kwallon kafar wadancan nahiyoyin biyu da lafin karbar cin hanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.