Isa ga babban shafi
FIFA

Sai an maimaita wasan Afrika ta kudu da Senegal- FIFA

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta bukaci a maimaita wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da aka fafata tsakanin Afrika ta kudu da Senegal bayan samun alkalin wasan da yin coge.

Sadio Mané na Senegal a lokacin da suke fafatawa da Afrika ta kudu a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha
Sadio Mané na Senegal a lokacin da suke fafatawa da Afrika ta kudu a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha STRINGER / AFP
Talla

FIFA ta dakatar da Alkalin wasan dan Ghana Joseph Lamptey har abada bayan ya yi coge a alkalancin wasan da Afrika ta kudu da Senegal suka buga a watan Nuwamban 2016.

Afrika ta kudu ce ta yi nasara da ci 2-1 bayan alkalin ya ba kasar wani fanariti da har ya janyo aka dakatar da shi.

Matakin maimata wasan dai yanzu na zuwa a yayin da Senegal ke matsayi na uku a rukuninsu na D a yayin da kuma ya rage wasanni biyu.

A watan Nuwamba mai zuwa kasashen biyu za su sake fafatawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.