Isa ga babban shafi
Wasanni

Barcelona ta cimma matsaya da Dortmund a kan Dembele

Kungiyar Barcelona ta cimma matsaya da takwararta ta Borussia Dortmund domin sayan dan wasanta Ousmane Dembele kan kudi fam miliyan 97.

Ousmane Dembele na kungiyar Borussia Dortmund a ranar 9 ga watan Agustan 2017.
Ousmane Dembele na kungiyar Borussia Dortmund a ranar 9 ga watan Agustan 2017. REUTERS/Wolfgang Rattay
Talla

Dembele mai shekaru 20, wanda kuma da wasan gaba ne na tawagar kwallon kafar kasar Faransa, zai isa Barcelona ne a ranar Lahadi, yayinda kuma za’a gwada lafiyarsa a ranar Litinin, kafin daga bisani ya sanya hannu kan yarjejeniyar bugawa kungiyar wasanni, tsawon shekaru biyar.

Kungiyar Barcelona ta warewa Dembele riga mai dauke da lamba 11.

Dembele shi ne dan wasan gaba na farko da Barcelona ta saya, tun bayan tafiyar Neymar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.