Isa ga babban shafi
Wasanni

Neymar ya soki salon shugabannin Barcelona

Dan wasa mafi tsada a duniya Neymar JR, ya soki shugabancin tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona, inda y ace, wadanda suke rike da mukaman daraktocin kungiyar basu cancanta ba, don a ganinsa salonsu ba zai haifarwa da kungiyar da mai idanu ba.

Dan wasa mafi tsada a duniya na Kungiyar PSG ta Faransa Neymar JR.
Dan wasa mafi tsada a duniya na Kungiyar PSG ta Faransa Neymar JR. Foto: REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Neymar ya bayyana haka ne yayinda suka kammala wasa tsakaninsu da kungiyar Toulouse, inda ya taimakawa kungiyarsa ta PSG jefa kwallaye 2 daga cikin 6 da ta zurawa Toulouse a ranar Lahadin da ta gabata.

Sai sai a cewar Neymar duk da haka ya ji dadin shekaru hudun da ya kwashe yana bugawa Barcelona wasanni.

A halin da ake ciki, duk da dafe makudan kudaden da kungiyar ta yin a Saida Neymar, har yanzu bata cimma burin maye gurbinsa, kasancewar har yanzu, tana kan kokarin sayo ‘yan wasan da suka hada da Philippe Coutinho na Liverpool da kuma Ousmane Dembele na Borussia Dortmund.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.