Isa ga babban shafi
Wasanni

Neymar zai isa Paris a wannan alhamis don kulla kwantaragi da PSG

A wannan alhamis Neymar zai isa birnin Paris na Faransa a shiye-shiryen sanya hannu kan sabon kwantaraginsa da PSG a kan kudi Euro milyan 222, kimanin dala milyan 260, wanda hakan zai kawo karshen zamansa a Barcelona.

Neymar avant son arrivee a PSG
Neymar avant son arrivee a PSG © AFP
Talla

An dai share tsawon kwanaki ana jita-jita dandange da wannan ciniki wanda a halin yanzu ya zama gaskiya, inda da farko Neymar mai shekaru 25 ya je wani asibiti da ke birnin Porto inda aka duba lafiyarsa tukuna, inda wani lokaci a yau zai isa birnin na Paris.

Za a gabatar da shi ga magoya bayan sabon kulob dinsa na Paris Saint Germains a ranar asabar mai zuwa, lokacin da wannan kulob zai buga wasansa na farko da Amiens a gasar Ligue ta Faransa da za a buda.

To sai dai a cikin wadannan kudade Euro milyan 222 da ake cewa an sayo dan wasan, duka duka zai tashi ne da abinda bai wuce Euro milyan 32 ba a shekara.

A ranar laraba ne shugabannin tsohon kulob din da ya ke bugawa Barcelona, suka tabbatar da cewa lalle sun rasa dan wasan, duk da cewa sun yi iya kokarinsu domin ganin cewa bai bar su ba.

Neymar dai ya fara buga wa Barcelona ne tun a 2013.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.