Gasar wasannin kasashe renon Faransa a birnin Abidjan
Wannan juma’a ake bude gasar wasannin kasashen renon Faransa karo na 8 a kasar Cote d’Ivoire, wasannin da za a ci gaba da gudanarwa har zuwa ranar 30 ga wannan wata na yuli.
Wallafawa ranar:
Shekaru 30 da farawa, sai a wannan ne Cote d’Ivoire ke daukar nauyin shirya gasar, inda ‘yan wasa daga kasashe kusan 80 suka hallara.
Za a bude gasar ce a daidai lokacin da kasar ke farfadowa daga matsalar yajin aiki, boren soji da kuma nuna wa duniya cewa kasar za ta iya daukar nauyin wasannin kasa da kasa, a matsayinta na kasar da za ta shirya gasar neman kofin kwallon kafar Afirka a 2021 idan Allah ya kai mu.
Cote d’Ivoire ta zama kasa ta hudu da ke daukar nauyin wannan gasa ta Francophonie a Afirka, bayan ga birnin Rabat na kasar Maroko a 1989, Antananarivo na Madagascar a 1997, sai Yamai a jamhuriyar a 2005.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu