Dan wasan ya ce yana fatar kafa tarihi idan ya lashe kofin zakarun Turai da Paris Saint Germaine.
An yi zaton dan wasan zai koma Manchester City City domin sake haduwa da tsohon kocinsa Pep Guardiola da ya horar da shi a Barcelona.
Amma Alves ya yi watsi da bukatar bayan PSG ta taya shi fiye da kudaden da City ta ce zata bashi.
Dan wasan zai karbi kudi euro miliyan 14 a duk shekara.