Isa ga babban shafi
Wasanni

Kotu ta yi watsi da daukaka karar Platini

Kotun kolin kasar Switzerland ta yi watsi da daukaka karar tsohon shugaban hukumarkwallon kafar nahiyar turai, Michel Platini, inda ya bukaci kotun ta soke hukuncin da ya haramta mishi shiga dukkanin wasu al’amuran wasanni tsawon shekaru hudu.

Tsohon shugaban hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar turai UEFA, Michel Platini.
Tsohon shugaban hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar turai UEFA, Michel Platini. REUTERS/Ruben Sprich/File
Talla

Kwamitin da’a na hukumar FIFA ne ya haramtawa Platini shiga dukkanin al’amuran wasanni na tsawon shekaru 4 saboda samunsa da laifin karbar na goro da yawansa ya kai dala miliyan 2, wanda tsohon shugaban hukumar FIFA Sepp Blatter ya bashi a shekarar 2011.

Hakan yasa kwamitin da’ar ya haramtawa Blatter da kuma Platini shiga al’amuran wasanni saboda samunsu da ya yi da laifin saba ka’ida.

Ko a shekarar data gabata sai da babbar kotun kasar Switzerland da ke sauraron kararraki kan wasanni ta tabbatar, haramcin da aka yi wa Platini.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.