Isa ga babban shafi
Wasanni

FIFA ta haramtawa kasar Sudan shiga wasanni

Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA, ta dakatar da kasar Sudan, daga shiga dukkanin wasannin kwallon kafa a ciki da wajen Nahiyar Afrika.

Shugaban hukumar FIFA, Gianni Infantino.
Shugaban hukumar FIFA, Gianni Infantino. AFP
Talla

Cikin sanarwar data fitar a yau Juma’a FIFA ta ce, matakin da ya dauka ya biyo bayan kutsen da gwamnatin Sudan ta yi a cikin al’amuran tafiyar da hukumar kwallon kafar kasar ba bisa ka’ida ba.

FIFA ta ce dole ne gwamnatin Sudan ta maido da shugaban hukumar kwallon kafar kasar Mu’tasim Ja’afar, bisa matsayinsa bayan korar sa da ta yi da ma ilahirin daraktocinsa, in data maye gurbinsa da AbdelRahman Elkatim a ranar 2 ga watan Yuni da ya gabata.

Tun a ranar 27 ga watan Yunin hukumar FIFA ta umarci gwamnatin Sudan ta soke umarnin data bayar kafin karshen watan; umarnin da Sudan din ta hau kujerar naki a kansa, dalilin kenan daya sanya FIFA daukar tsattsauran matakin a kan sha’anin kwallon kafar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.