Isa ga babban shafi
Wasanni-Tennis

Gasar Wimbledon: Wawrinka ya fice a zagayen farko

Zakaran gasar kwallon Tennis mai rike da kafunan wasannin Grand slam har sau uku, Stan Wawrinka, ya fice daga gasar Wimbledon da ke gudana a birnin London a zagayen farko.

Stan Wawrinka na kasar Switzerland a lokacin da Daniil Medvedev na Rasha ya fitar da shi daga gasar kwallon Tennis ta Wimbledon.
Stan Wawrinka na kasar Switzerland a lokacin da Daniil Medvedev na Rasha ya fitar da shi daga gasar kwallon Tennis ta Wimbledon. REUTERS
Talla

Wawrinka dan kasar Switzaerland, da ke mataki na uku wajen matakin kwarewa a wasan kwallon Tennis din a duniya, yayi rashin nasara ne a hannun Daniil Medvedev dan kasar Rasha, da kwallaye 6-4, 3-6, 6-4, sai kuma 6-1.

Karo na farko kenan da Medvedev mai shekaru 21 kuma dan wasan kwallon tennis na 49 a duniya, ya ke buga gasar ta Wimbledon.

Ba dai wannan bane karo na farko da ake fitar da shaharrun ‘yan wasan kwallon tennis daga wasanni daban daban da suke bugawa ba.

Ko a ranar 21 ga watan Yuni sai da aka fitar da Andy Murray dan kasar Birtaniya, daga gasar wasan kwallon Tennis ta Aegon da ke Gudana a Birmingham tun a zagayen farko, wanda kuma shi ke rike da kofin gasar.

Kuma wanda ya samu nasarar yin waje da Murray, wato Jordan Thompson dan kasar Australia, yana a matsayi na 90 ne, a matakin kwarewa, tsakanin jerin ‘yan wasan kwallon Tennis a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.