Isa ga babban shafi
Wasanni

United ta fi dacewa da Ronaldo - Meireles

Dan wasan kwallon kafar kasar Portugal Raul Meireles ya shawarci takwaransa Cristiano Ronaldo cewa, babu inda ya dace ya koma murza kwallon kafa idan har ya zartas da matakin barin Real Madrid kamar tsohuwar kungiyarsa ta Manchester United.

Cristiano Ronaldo mai rike da kambun gwarzon dan wasan kwallo kafa na duniya
Cristiano Ronaldo mai rike da kambun gwarzon dan wasan kwallo kafa na duniya Reuters/Kai Pfaffenbach
Talla

A makon da ya gabata ne wasu majiyoyi suka rawaito cewa Ronaldo yana son komawa tsohuwar kungiyarsa ta Manchester United, bayanda hukumomin Spain suka zargi dan wasan da kin biyan haraji Euro miliyan 14. Abinda bai yiwa Ronaldo dadi ba.

Bayan kammala gasar cin kofin kalubale na zakarun kasashe daga nahiyoyin Duniya, ake sa ran Ronaldo ya tattauna da shugaban Kungiyar Real Madrid, Florentino Perez, dangane da yiwuwar cigaba da zaman nasa a kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.