Isa ga babban shafi
Wasanni

Riyad Maharez zai raba gari da Leicester City

Dan wasan tsakiya na kungiyar Leicester City, Riyad Maharez, ya amince da sauya sheka zuwa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a kan kudi fan miliyan 35.

Dan wasan tsakiya na kungiyar Riyad Mahrez
Dan wasan tsakiya na kungiyar Riyad Mahrez dailymail
Talla

A watannin baya, rahotanni sun tabbatar da cewa kungiyar Barcelona, ta yi kokarin saye shi daga Leicester, amma daga bisani maganar ta lafa.

Tayin farko da kungiyar Arsenal ta yiwa Maharez, shi ne na rattaba hannu kan yarjejeniyar buga mata  wasanni, tsawon shekaru hudu, wanda kuma ya amince da hakan.

A makon da ya gabata, an rawaito cewa dan wasan gaba na Arsenal Alexis Sanchez, ka iya sauya sheka zuwa kungiyar Manchester City, wanda hakan yasa wasu masharhanta ke ganin zai iya haifar wa da Arsenal nakasu wajen zura kwallaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.