Isa ga babban shafi
Wasanni

Spain na zargin Mourinho da kin biyan haraji

Masu shigar da kara na Spain na zargin Kocin Manchester United Jose Mourinho da kauce wa biyan haraji a lokacin da ya ke horar da kungiyar Real Madrid.

José Mourinho na Manchester United
José Mourinho na Manchester United Oli SCARFF / AFP
Talla

Ana zargin Mourinho da damfarar Spain kudaden haraji da yaewansu ya kai Euro miliyan 3.3 kwatankwacin Dalar Amurka miliyan 3.6 tsakanin shekarar 2011 da 2012.

Masu shigar da karar sun ce, Mourinho ya ki bayyana kudaden shigarsa kamar yadda doka ta tanada, abin da ya ba shi damar awon gaba da haramtattun kudade.

Kawo yanzu dai Mourinho bai ce uffam ba game da wannan sabon zargin da ya kunno kai bayan wanda aka yi gwarzon dan wasan duniya, Christiano Ronaldo.

Ana zargin Ronaldo da kin biyan harajin Euro miliyan 14.7

A bangare guda, shugaban Real Madrid Florentino Perez ya bayyana cewa, kawo yanzu bai gana da Ronaldo ba game da makomarsa a kungiyar, amma ya ce, zai gana da shi bayan kammala gasar zakarun nahiyoyin duniya.

Wannan na zuwa ne bayan Ronaldo ya ce, yana son kawo karshen taka ledarsa a Spain sakamakon zargin kauce wa biyan harajin.

Ana rade-radin cewa, gwarzon dan wasan mai shekaru 32 zai koma Manchester United.

Tuni dai hukumomin Spain suka sanya ranar 31 ga watan gobe a matsayin ranar da Ronaldo zai bayyana a gaban kotun Madrid don amsa tambayoyi kan zarge-zarge hudu na kauce wa biyan harajin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.