Isa ga babban shafi
Wasanni

Modric na fuskantar tuhuma bisa bada shaidar karya

Dan wasan tsakiya na kungiyar Real Madrid, Luca Modric, yana fuskantar tuhuma a kasarsa Crotia bisa zargin bada bayanan karya, a wata shaida da ya bayar gaban kotu.

Croatia and Real Madrid midfielder Luka Modric appears in court to testify in a corruption trial in Osijek on June 13, 2017.
Croatia and Real Madrid midfielder Luka Modric appears in court to testify in a corruption trial in Osijek on June 13, 2017. AFP
Talla

Jami’ai a Crotia sun kaddamar da bincike kan Modric, bisa zarginsa da ake na bada shaidar Zur, a shara’ar da ake yiwa tsohon mai horar da shi a kungiyar Dinamo Zagreb, wato Zdravko Mamic, wadda wata kotun musamman ke saurara a birnin Osijek dangane da aikata almundahana yayin da yake Klub din na Dinamo Zagbreb a watan Yulin shekara ta 2004.

Ana dai zargin tsohon mai horar da kungiyar ta Dinamo Zagreb, Mamic, da laifin hadin baki da wasu jami’ai biyu da kuma wani kaninsa, a lokacin da yake horar da kungiyar, inda suka sace akalla euro miliyan 15 daga bital malin kungiyar, ta hanyar bayar da kwangiloli na karya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.