Isa ga babban shafi
Wasanni

FIFA: Allura ta tono garma

Kwamitin da’a na hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA, ya fara bincikar zargin da ake wa shugaban hukumar, Gianni Infantino na yin amfani da kujerarsa, wajen tasiri a kan sakamakon zaben shugabancin hukumar lura da kwallon kafar nahiyar Afrika.

Shugaban hukumar FIFA, Gianni Infantino.
Shugaban hukumar FIFA, Gianni Infantino. Reuters / Matthew Childs
Talla

Babban mai shigar da kara na Kotun wasanni da ke Switzerland Cornel Borbely, kuma shugaban kwamitin da’ar na FIFA, ya ce kaddamar da binciken, ya biyo bayan, wasu shaidu da aka gabatar musu, kan yadda Infantino ya taka rawa wajen tabbatar da an zabi Ahmad Ahmad na Madagascar a matsayin shugaban hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF watan Maris.

A ranar Lahadin da ta gabata, Jaridar the Guardian ta Birtaniya, ta rawaito wasu majiyoyi da ke cewa, kafin zabukan, Infantino da sakatariyar hukumar ta FIFA Fatma Samoura, sun yi alkawarin cewa hukumomin lura da kwallon kafa na kasashen nahiyar Africa, zasu rika yin kwanciyar magirbi kan damin damasheren kudade, fiye da wanda hukumar ta FIFA ke ware musu a baya, muddin wakilansu suka zabi Ahmad Ahmad ya taka takara, ya kuma samu nasara.

Zalika majiyoyin sun ce Infantino ya dauki matakin ne, domin ya kawar da Issa Hayatou daga shugabancin hukumar CAF, kasancewar Hayatou bai goyi bayan takararsa ba, a lokacin da ya nemi darewa kujerar shugabancin hukumar ta FIFA.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.