Sampaoli zai zama kocin Argentina
Argentina na shirin ba Jorge Sampaoli aikin horar da ‘yan wasan kasar bayan kungiyar Sevilla ta tabbatar da cim ma yarjejeniya tsakaninta da hukumar kwallon kafar kasar.
Wallafawa ranar:
Sampaoli ya yi kokarin kai Sevilla matsayi na hudu a teburin La liga a bana a cikin shekara daya da ya karbi aikin horar da kungiyar.
Argentina dai na fuskantar barazanar kasa tsallakewa zuwa gasar cin kofin duniya a karon farko tun a 1970.
Zuwan Argentina gasar cin kofin duniya a Rasha ne babban kalubalen da ke gaban Sampaoli bayan ta sha kashi hannun Bolivia a watan Maris.
Argentina na matsayi na biyar ne a teburin kasashen kudancin Amurka, kuma kasashe hudu ne kawai ke da hurumin zuwa gasar cin kofin duniya da za a gudanar a Rasha a 2018.
Sampaoli zai fara jagorantar Argentina a wasan sada zumunci tsakaninta da Brazil a 9 ga Yuni, kafin wasa da Uruguay a Agusta domin neman shiga gasar cin kofin duniya
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu