Isa ga babban shafi
Wasanni

Real Madrid ta lashe gasar La liga

Real Madrid ta yi nasarar lashe kofin sakamakon nasarar da ta samu a kan Malaga da ci 2-0.Wannan dai shine karo na 33 da kungiyar ta samu nasara lashe kofin kuma na farko tun a shekara ta 2012.

Tawagar Real Madrid da suka daga kofin La Liga
Tawagar Real Madrid da suka daga kofin La Liga Reuters / Jon Nazca
Talla

Kungiyar ta kakkare lig din na la liga da maki 93, abokiyar hamayarta Barcelona da maki 90, banbancin maki uku a tsakani.

Yanzu kuma Real Madrid na jiran wasan karshe na cin kofin kungiyoyin zakarun nahiyar turai a ranar 3 ga watan yuni da zata kara da Juventus.

Idan har kungiyar ta samu nasara zai kasance karon farko a gasar tun bayan da aka canza mata suna zuwa kofin zakaru da wata kungiya zata ci ta kuma sake maimaita ci a shekara ta gaba.

Sakamakon sauran wasanni la liga da aka buga

Barcelona 4-2 Eibar

Celta vigo 2-2 Real Sociedad

Atletico Madrid 3-1 Bilbao

Valencia 1-3 villareal

Sevilla 5-0 osasuna

Deportivo- 3-0 Las palmas

Granada 1-2 Espanyol

Gijon 2-2 Real Betis

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.