Isa ga babban shafi
Wasanni

Real Madrid na gab da lashe gasar La liga

Real Madrid na gab da lashe gasar La liga a karon farko cikin shekaru biyar sakamakon nasarar da kungiyar ta samu a wasan da ta buga da Celta Vigo jiya laraba, inda ta lallasa ta, ci 4-0.

Dan wasan tsakkiyar fagen kungiyar Real Madrid Cristiano Ronaldo
Dan wasan tsakkiyar fagen kungiyar Real Madrid Cristiano Ronaldo Reuters / Paul Hanna Livepic
Talla

Yanzu kungiyar ta bai wa abokiyar hamayyar ta Barcelona tazarar maki Uku inda yanzu ta ke da maki 90 yayin da ita kuma Barcelona ke da 87.

Wasa daya ya rage a karkare La ligan kuma ko da kunne doki Real Madrid ta buga, a wasan karshen da zata ziyarci Malaga, ta lashe gasar.

Cristiano Ronaldo ya samu nasarar sa kwallaye har biyu a wasan, wanda haka ya bashi damar kafa tarihi a matsayin dan wasan da yafi kowa cin kwallaye a manyan lig na nahiyar turai biyar, inda yanzu ya ke da kwallaye 368 kuma ya wuce wanda ke rike da tarihin Jimmy Greaves na kasar Ingila.

Toh sai dai acan Ingila, Manchester united ce ta buga kunnen doki a wasan da ta kara da Southampton a jiya Laraba bayan dauki ba dadi da aka yi domin duk wanda ya kalli wasan yasan cewa ko wacci zomo ya ci gudu.

Manchester ta buga wasan ne ba tare da wasu daga cikin manyan ‘yan wasan ta ba saboda raunin da wasu ke fama da shi da kuma hutun da aka ba Paul Pogba saboda rasuwar mahaifin sa.

Dan wasan da yafi kwazo a wasan dai shine mai tsaron gida na Manchester United, Sergio Romero wanda ya ture fenaritin da Manolo na Southampton ya buga,

Sannan kuma ko acikin wasan Romero ya ta nuna bajin ta, za’ a ma iya cewa shi ya hana Southampton samun nasara a wasan.

Yanzu dai Manchester na jiran wasan karshe na cin kofin Europa da zata kara da Ayax domin sanin ko zata iya shiga gasar cin kofin kungiyoyin zakarun nahiyar turai ko a’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.