Isa ga babban shafi
Wasanni

Monaco ta daga kofin Ligue 1 karon farko a shekaru 17

Kungiyar Monaco ta daga kofin Ligue 1 na Faransa a karon farko cikin shekaru 17. Kylian Mbappe ne ya fara zura kwallon farko da ke kasancewa kwallo ta 15 da ya ke ci a wannan kaka a fafatawar da ta doke Saint-Etienne ci 2-0.

Monaco ta daga kofin Ligue 1 na Faransa
Monaco ta daga kofin Ligue 1 na Faransa Reuters / Jean-Pierre Amet
Talla

Kwallon Mbappe ne ya rike ta na tsawon lokaci ana kece raini, Kana ana gab da tashi Valera Germain ya rufe wasa da kwallon karshe.

Kaptain din kungiyar Radanel Falcao ya ce wannan baban nasara ce a tarihin kungiyar.

Tun a fafatawarsu ta ranar Lahadi da suka doke Lille ci 4-0 aka yanke suna iya daukan wannan kofi la’akari da cewa maki guda suke bukata.

Nasaran Monaco a wasanni 11 a jere ya bata daman samun maki 92 a teburi, banbanci maki 6 da PSG, kuma suna iya kafa tarihi nasaran a wasanni 30 idan suka doke Rennes a wasan karshe ranar Assabar.

Yanzu dai tauraron Mbappe na haskawa wanda ke tsokallewa wasu daga cikin manyan kungiyoyin Ingila Ido.

A Italiya kuwa, Juventus ce ta sami nasarar doke Lazio ci biyu da nema a gasar Coppa Italiya.

Kungiyar ta sami nasarar saka kwallayen biyu ta hannun masu tsare mata baya wato Dani Alves da Leanardo Bonucci.

Kafin wannan wasa Juventus ta sami nasarar lashe gasar Serie A, kuma ta na jiran wasan karshe na cin kofin kungiyoyin zakarun nahiyar turai da zata kara da Real Madrid a watan Yuni.

Kocin kungiyar, Allegri ya ce nasarar ta kara masu karfi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.