Tawagar tseren gudun Najeriya ta gaza kare kambunta
Tawagar Najeriya ta gaza kare Kambunta na lambar zinare a gasar bana ta tseren gudu ta duniya.
Wallafawa ranar:
Tawagar dai ta wakilci Najeriya ne a gasar tseren gudun na mita 200, mai kunshe da ‘yan wasa 4, ciki harda Blessin Okagbare, inda tawagar ta kammala a matsayi na biyar, cikin miniti 1 da dakika 33 da digo 8.
Yayin gasar da ta gudana a shekara ta 2015, tawagar Najeriya ta kammala tseren mita dari biyun cikin minti 1 da dakika 30 da digo 52.
A wannan karon dai kasar Jamaica ce ta lashe lambar zinare, sai kuma Jamus mai biye mata da Lambar azurfa yayinda Amurka ta lashe lambar tagulla sai kuma kasar Trinidad and Tobago a matsayi na 4.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu