Isa ga babban shafi
Wasanni

Terry zai raba gari da Chelsea

Dan wasan Chelsea John Terry zai raba gari da kungiyar a karshen wannan kakar da muke ciki kamar yadda kungiyar da ke jagorantar teburin gasar Premier ta Ingila ta sanar.

John Terry ya shafe kimanin shekaru 20 a Chelsea
John Terry ya shafe kimanin shekaru 20 a Chelsea REUTERS/Stefan Wermuth
Talla

Terry mai shekaru 36 kuma tsohon dan wasan tawagar Ingila, ya buga wa Chelsea wasanni 713, abin da ya sa ya kasance dan wasa na uku da ya fi buga wa kungiyar wasanni a tarihinta bayan Ron Harris da Peter Bonetti.

Duk da cewa, shi ne kaften a kungiyar, kocin Chelsea na yanzu Antonio Conte bai ba shi fifiko wajen sanya shi a tawagar da ke buga ma sa tamaula, domin kuwa wasanni biyar kacal ya buga wa kungiyar a wannan kakar a gasar League.

Terry da ya shafe kimanin shekaru 20 a Chelsea, ya ci ma ta kwallaye 66, yayin da ya lashe ma ta kofunan Premier hudu da kofunan FA biyar da kofin Europa daya da League Cup uku.

A shekara 2012 ne, John Terry ya yi ritaya daga buga wa kasarsa ta Ingila tamaula bayan ya buga ma ta wasanni 78.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.