Isa ga babban shafi
Wasanni

Arsenal na fatan kammala Premier a saman teburi

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta farfado da damarta ta kammala gasar Premier a jerin kungiyoyi hudu da ke saman teburi bayan ta samu nasarar doke Middlesbrough da ci 2-1 a kece rainin da suka yi a jiya Litinin. 

Kocin Arsenal Arsene Wenger
Kocin Arsenal Arsene Wenger Reuters/Matthew Childs
Talla

Alexis Sanchez ne ya fara zura kwallon farko a minti na 42 da soma wasa, yayin da Alvaro Negredo ya farke wa Middlesbrough jim kadan da dawowa daga hutun rabin lokaci.

Sai dai gabanin a tashi wasan, Mesut Ozil ya sake jefa kwallo guda a ragar Middlesbrough.

Ozil dai shi ne ya sama wa Arsenal maki ukun da take tsananin bukata.

A halin yanzu, Arsenal na mataki na 6 a teburin gasar Premier kuma akwai tazarar maki 7 tsakaninta da Manchester City da ke mataki na hudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.