John Terry zai bar Chelsea
Chelsea ta sanar cewa kaftin din ta John Terry zai bar kungiyar a karshen kaka bayan ya shafe shekaru 22 yana murza leda a kungiyar. Terry ya yi haskawa 713 a Chelsea tare da jefa kwallaye 66 a raga.
Wallafawa ranar:
Dan wasan ya shafe shekaru 22 a Chelsea tun 1998. Shi ne dai dan wasa na uku a tarihin kungiyar da ya fi haskawa a kungiyar.
Duk da dai Terry ne kaftin na Chelsea amma kocin kungiyar na yanzu Antonio Conte ba ya amfani da shi inda wasanni 5 kacal ya buga a kakar bana.
Dan wasan ya ce nan gaba zai sanar da makomar shi.
Terry ya lashe kofunan gasar premier 4 a Chelsea da kofunan FA guda 5 da kofin kalubale na ingila guda uku.
Sannan ya lashe kofin zakarun Turai a 2012 zamanin Di Matteo da Kofin europa a zamanin Rafael Benitez
Terry ya ce yana fatar dawo wa Chelsea amma ba a matsayin dan wasa ba idan ya rataye takalminsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu