Wasanni
Dalilan da ke sa wasu shahararrun 'yan kwallo na komawa Amurka da China
Wallafawa ranar:
Kunna - 09:56
Mafi yawa daga cikin shahrarren 'yan wasa musamman a fagen kwallon kafa, na kulla kwantaragi domin buga wa wasu kungiyoyi da ke China ko kuma Amurka.To sai dai abin lura a nan shi ne mafi yawansu na kulla irin wannan kwantaragi ne a daidai lokacin da suka fara shiga shekarun gaf da yin ritaya daga kwallon kafa, yayin da wasu ke daukar irin wannan mataki saboda yadda taurarinsu suka fara dushewa.A cikin na wannan mako, AbdurRahman Gambo Ahmed ya yi mana dubi a game da wannan batu.