Isa ga babban shafi
Ingila

Magoya bayan Arsenal na son a raba gari da Wenger

Kashin da Arsenal ta sha a jiya hannun Crystal Palace ya dada farfado da yekuwar korar Arsene Wenger da bagoya bayan kungiyar ke yi.

Kocin Arsenal Arsene Wenger
Kocin Arsenal Arsene Wenger Reuters/Stefan Wermuth
Talla

Arsenal ta sha kashi ne ci 3-0, wanda ya kara nutse kungiyar da tazarar maki 7 tsakaninta da matsayi na hudu a teburin Firimiya, rukunin zuwa gasar cin kofin zakarun Turai.

Kashin da Arsenal ta sha a Selhurst Park a jiya shi ya mamaye kanun labaran wasanni na jaridun Birtaniya.

Sai dai kuma wani labarin marar dadi ga masoya Arsenal din shi ne yadda kafofin yada labaran Birtaniya suka ruwaito cewa Arsene Wenger na shirin sanya hannu kan sabuwar kwangilar ci gaba da horar da kungiyar.

Tun a 1996 Wenger ke horar da Arsenal, kuma duk shekara sai ya kai kungiyar gasar zakarun Turai.

Amma alamu na nuna yana da wahala Arsenal ta samu huruminta na zuwa gasar zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.