Isa ga babban shafi
Rasha

Confederation Cup: Ana kauracewa sayen tikiti a Rasha

Rasha ta bayyana damuwa kan yadda ake kauracewa sayen tikitin shiga kallon gasar cin kofin kalubale na zakarun kasashen nahiyoyin duniya da za gudanar tsakanin watan Yuni zuwa Yulin bana.

Vladimir Putin shugaban Rasha
Vladimir Putin shugaban Rasha REUTERS
Talla

Wani kamfanin dillacin labaran wasanni R Sport ya ambato Firaministan Rasha Vitaly Mutko na bayyana damuwa kan rashin cinikin tikitin shiga kallon wasannin.

Daga cikin tikici dubu dari bakwai da Rasha ke son sayarwa, yanzu tikici dubu dari biyu ne aka sayar yayin da lokacin gasar ke karatowa.

Wannan dai alamu ne da ke nuna gasar ba za ta yi armashi ba a Rasha, har ma da gasar cin kofin duniya da kasar zata karbi bakunci a badi.

Kasashen da za su fafata sun hada da Rasha mai masaukin baki da Jamus da ta lashe kofin duniya.

Sai kuma Portugal da ta lashe kofin Turai da Kamaru da ta lashe kofin Afrika da Chile da ta lashe Copa Amerika na kudancin Amurka da Mexico da ta lashe na arewa da tsakiyar Amurka da Caribbean da Australia da ta lashe kofin yankin Asia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.