Isa ga babban shafi
Wasanni

Moyes zai amsa tambaya kan marin 'yar jarida

Hukumar Kwallon Kafar Ingila za ta tambayi kocin Sunderland David Moyes don ya yi ma ta bayani game da kalaman da ya furta wa wata ‘yar Jarida, in da ya ce ma ta za ta iya shan mari, in ba ta yi taka-tsan-tsan ba.

David Moyes na Sunderland
David Moyes na Sunderland REUTERS/Phil Noble
Talla

Bayan kammala wasan da Sunderland ta tashi kunnen doki 1-1 da Burnely a ranar 18 ga watan Maris da ya gabata, ‘yar Jaridar mai suna Vicki Sparks ta yi hira da Moyes, in da ta tambaye shi ko halartar mamallakin kungiyar ta Sunderland, Ellis Short don kallon wasan ya kara masa matsin lamba.

Sai ya ce ma ta a’a, amma bayan kammala hirar sai Moyes ya ce wa ‘yar Jaridar da yiwuwar ki sha mari duk da cewa  ke mace ce don haka ki yi taka-tsan-tsan nan gaba.

Sai dai daga bisani Kocin ya yi nadamar furta kalaman nasa kuma ya bai wa ‘yar jaridar hakuri.

Amma duk da haka Hukumar Kwallon Kafar Ingila za ta rubuta wa Moyes wasika don yi ma ta bayani kan wannan batu da wasu ke kallo tamkar nuna kaskanci ga mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.