An haramtawa FC Rostov amfani da filin wasanta
Mako guda bayan da mai horar da kungiyar Manchester United Jose Mourinho ya koka bisa rashin kyawun yanayin filin wasa na kungiyar FC Rostov da suka fafata wasa da ita a ranar Alhamis, hukumar kwallon kafar Rasha ta haramtawa kungiyar amfani da filin.
Wallafawa ranar:
Hukumar ta kuma bai wa kungiyar ta FC Rostov wa’adin zuwa ranar 24 ga watan Maris domin gyara yanayin filin kwallon kafar da ke kama da gonar da ake shirin yi wa huda.
A wasan da ya gudana dai an tashi ne 1-1 tsakanin Manchestern da Rostov,kuma kafin wasan Mourinho ya koka bisa rashin kyawun filin kungiyar, inda bayan wasan ya ce dalilin da ya sanya ‘yan wasansa gaza raba kwallo dalla dalla tsakaninsu kenan har ta kaisu ga tashi kunnen doki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu