Isa ga babban shafi
Champions League

Bayern Munich ta sake lallasa Arsenal

Bayern Munich ta sake ba Arsenal kashi ci 5-1 a Emirate kamar yadda ta lallasa ta a Allianz Arena Jamus. Karo na 7 ke nan a jere ana yin waje da Arsenal a zagaye na biyu na gasar zakarun Turai.

Magoya bayan Arsenal sun gaji da Arsene Wenger
Magoya bayan Arsenal sun gaji da Arsene Wenger REUTERS
Talla

A jiya dai Arsenal ta sha kashin da ba ta taba sha ba a filin wasanta na Emirate.
Arsene Wenger da ya shafe shekaru sama da 20 yana kocin kungiyar, a jiya ya fuskanci bore daga wasu magoya bayan Arsenal, tun kafin ma a fara wasan.

Kuma bayan alkali ya hure wasan, magoya bayan Arsenal sun ta daga tuta da kwali da ke kiran a kori Arsene Wenger.

Bayern Munich dai ta kai zagayen kwata fainal a yanzu da jimillar kwallaye 10-2.

Yadda Bayern ta yi kaca kaca da Arsenal, shi ne ya mamaye kanun labaran wasanni a jaridun Birtaniya.

Jaridar Daily Express ta buga babban labarinta mai taken “An sake yin abin kunya”.

Daily Telegraph kuma ta buga cewa “An kunyata Arsenal, magoya bayan kungiyar sun bukaci Wenger ya yi murabus”.

Real Madrid da Napoli

Real Madrid ta kai zagayen kwata fainal bayan ta sake doke Napoli ci 3-1.

A jiya Napoli ce ta fara jefa kwallo a raga, amma Sergio Ramos ya farke kwallon tare da jefa kwallo ta biyu kafin Morata ya jefa kwallo ta uku.

Real ta kai zagayen kwata fainal da jimillar kwallaye 6-2, yayin da take farautar kare kofin da ta lashe a bara.

Barcelona da PSG

A yau Barcelona za ta karbi bakuncin PSG da nnufin rama kwallaye 4.

Abubuwa dai za su kara rincabewa Barcelona Idan har PSG ta jefa mata kwallo a raga a gidanta.

Borussia Dortmund da Benfica

A Jamus Borussia Dortmund za ta karbi bakuncin Benfica tare da fatar rama kwallon da aka ci ta a Portugal.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.