Isa ga babban shafi
Najeriya-Wasanni

Martins ya bukaci a sake bashi dama a Super Eagles

Tsohon dan wasan Super Eagles ta Najeriya, Obafemi Martins, ya bukaci mai horar da ‘yan wasan kasar Gernot Rohr, ya bashi damar shiga cikin ‘yan wasan da zasu wakilci Najeriya a gasar cin kofin duniya da za’a yi a kasar Rasha, shekara ta 2018.

Obafemi Martins tare da Mikel Obi yayinda ya zura kwallo a ragar kasar Senegal a ranar 31 ga Janairu 2006.
Obafemi Martins tare da Mikel Obi yayinda ya zura kwallo a ragar kasar Senegal a ranar 31 ga Janairu 2006. goal.com
Talla

Obafemi wanda a yanzu ke kungiyar kwallon kafa ta Shanghai Shenhua a kasar China, ya ce har yanzu fa da sauran gudunmawar da zai bawa kasarsa a fagen kwallon kafa.

A cewar Martins League din kasar China da ke cigaba da jan shahararrun ‘yan wasa ba kanwar lasa bane, kamar yadda wasu ke raina shi.

An dai dauki tsawon lokaci ba  tare da jin duriyar tsohon dan wasan gaba na Najeriyar ba, tun bayan da ya koma kasar China da buga wasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.