Isa ga babban shafi
Wasanni

Najeriya ta ki goyon bayan tazarcen shugaban CAF Issa Hayatou

Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya NFF, ta ce tana goyon bayan ganin an samu sauyin shugabancin hukumar kula da kwallon kafa ta Nahiyar Afrika wato CAF.

Shugaban hukumar kula da kwallon kafa ta Nahiyar Afrika Issa Hayatou
Shugaban hukumar kula da kwallon kafa ta Nahiyar Afrika Issa Hayatou GHANAsoccernet
Talla

Wannan na zuwa yayinda shugaban hukumar ta CAF, Isa Hayatou, ya sake tsayawa takarar neman tazarce karo na 8, sai dai a wannan karon yana fuskantar hamayya daga shugaban hukumar kula da kwallon kafa ta kasar Madagascar, Ahmad Ahmad.

Shugaban hukumar NFF ta Najeriya, Amaju Pinnick, ya ce akwai bukatar ganin an samu sabon shugabanci, don samar da sabbin tsare tsare idan aka yi la’akari da yadda aka samu a matakin hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA.

Ko da yake Pinnick ya ce akwai yiyuwar Issa Hayatou yayi nasarar zarcewa, ya ce muddin yasamu nasarar yin haka, to fa ya zama tilas Hayatou ya tabbatar da kawo sauye sauye a salon tafiyar da kwallon kafa a Afrika.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.