Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Pogba zai fafata da yayansa a Old Trafford

Manchester United za ta karbi bakuncin Saint-Etienne a gasar Europa Lig a Old Trafford kuma haduwa ce tsakanin ‘Yan uwan juna guda biyu Paul da Florentin Pogba.

Man Utd zata kara da Saint-Etienne a Old Trafford wasan da zai hada Paul da yayansa Florentin Pogba
Man Utd zata kara da Saint-Etienne a Old Trafford wasan da zai hada Paul da yayansa Florentin Pogba francetvsport
Talla

Pogba da ke buga tsakiya a Manchester zai hadu ne da dan uwansa Florentin da ke tsare bayan Saint-Etienne.

Paul na Manchester mai shekaru 23 ya zabi bugawa Faransa wasa yayin da yayansa Florentin mai shekaru 26 ya zabi bugawa Guinea kwallo.

Florentin ya ce duk da cewa Manchester United babbar kungiyar ce amma za su yi kokarin ba su mamaki a Old Trafford.

Paul Pogba ne dan wasa mafi tsada a duniya wanda Manchester ta sayo daga Juventus akan kudi fam miliyan 89 da dubu dari uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.