Isa ga babban shafi
La liga

Sevilla ta doke Madrid bayan wasanni 40 tana nasara

Sevilla ta kawo karshen wasanni 40 da Real Madrid ta buga a jere da jere ba a samu galabarta ba, bayan ta samu sa’arta ci 2 da 1 a karawar da suka yi a gasar La liga a ranar Lahadi.

Sevilla ta doke Real Madrid ci 2-1 a La liga
Sevilla ta doke Real Madrid ci 2-1 a La liga REUTERS
Talla

Sergio Ramos ne ya ci kansu inda ya farke wa Sevilla kwallon da Cristiano Ronaldo ya fara jefawa Real Madrid.

Saura kiris a hure wasan kuma Stevan Jovetic ya jefa kwallon da ya ba Sevilla nasara a ragar Madrid.

Sevilla kuma yanzu na matsayi na biyu ne a teburin La liga, tazarar maki guda tsakaninta da Real Madrid da ke jagorancin teburin gasar. Kodayake tana da kwanten wasa.

Barcelona wacce ta casa Las Palmas 5-0 na matsayi na uku ne da tazarar maki guda tsakaninta da Sevilla.

Kocin Madrid Zinedine Zidane ya ce yana alfahari da tarihin da suka kafa na buga wasanni 40 suna nasara. Kuma a cewar shi hakan ba zai karye wa ‘yan wasan shi kwarin guiwa ba.

Rabon da a doke Madrid tun a watan Afrilun shekarar da ta gabata lokcin da Wolfsburg ta doke ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.