FIFA ta kare matakin fadada gasar kofin duniya
Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Gianni Infantino ya kare matakin da FIFA ta dauka na fadada gasar cin kofin duniya daga kasashe 32 zuwa 48.
Wallafawa ranar:
Infantino ya jaddada cewa, sun dauki matakin ne don kara daga martabar gasar ta cin kofin duniya amma ba wai don samun kudi ba kamar yadda wasu ke fadi musamman masu adawa da tsarin.
A jiya Talata ne mambobin hukumar ta FIFA suka kada kuri’ar amincewa da tsarin wanda zai fara aiki a shekarar 2026.
Yanzu haka dai za a rika gudanar da jumullar wasanni 80 a gasar a maimakon 64 da aka saba yi, sannan kuma za a rika kammala gasar a cikin kwanaki 32.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu